in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNDP da Global Fund za su hada gwiwa da Zimbabwe domin riga kafin cutar HIV
2016-09-01 09:59:21 cri

Shirin raya ci gaba na MDD UNDP, da asusun raya ci gaba na kasa da kasa Global Fund za su hada gwiwa don samar da dala miliyan 143, da nufin tallafawa shirin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV a kasar Zimbabwe.

Cutar HIV ta kasance babban kalubale game da sha'anin kiwon lafiya a kasar Zimbabwe, inda mutane miliyan 1 da dubu 400 ke dauke da kwayar cutar a bisa kididdiga a karshen shekarar 2015. Ko da yake, an samu raguwar yaduwar cutar ta HIV da kashi 15 cikin 100 a kasar, sai dai har yanzu kasar na sahun gaba cikin jerin kasashen duniya da cutar ta fi kamari.

Manufar samar da kudaden ita ce domin samun isassun magungunan cutar, da dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri, da samar da kayayyakin gwaje gwajen cutar, da kuma hanyoyi riga kafin yaduwar cutar a tsakanin matasan wadanda ba sa makaranta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China