in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar wani abu a wani gidan mai a Ghana ta halaka mutane 7
2016-12-23 10:41:27 cri

Jami'ai daga hukumar kashe gobara gami da kungiyar shawo kan annoba ta kasar Ghana, sun bayyana jiya Alhamis cewa, wani abu da ya fashe a wani gidan mai dake babbar cibiyar baje-koli ta kasa da kasa dake Accra, babban birnin kasar Ghana a daren jiya, ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 7, tare da raunata wasu 12.

Wasu ganau ba jiyau ba, sun ce bayan fashewar, wuta ta ruru har zuwa ginin babbar cibiyar baja-koli ta kasa da kasa.

Sai dai 'yan kwana-kwana sun kai dauki, inda suka shawo kan gobarar.

Har yanzu dai, ana ci gaba da binciken musabbabin gobarar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China