in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton MDD ya bayyana adadin fararen hula da suka mutu a hargitsin Afghanistan cikin 2016
2017-02-07 09:37:57 cri

A jiya ne MDD ta fitar da wani rahoto mai dauke da adadin fararen hula da suka mutu yayin hargitsin da suka faru a kasar Afghanistan cikin shekarar 2016, tana mai kira da a dauki matakan gaggawa na tsaron rayukan fararen hula a kasar.

Kakakin majalisar Stephane Dujarric ya ce, sabon rahoton da rundunar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar UNAMA ta fitar, ya nuna cewa, ba a taba samun makamancin adadin mutane da rikici ya rutsa da su cikin shekara guda ba kamar na bara, ciki har da adadin yara da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata.

A cewar rahoton na shekarar 2016, jimilar fararen hula dubu uku da dari hudu da casa'in da takwas ne suka mutu, yayin da wasu dubu bakwai da dari tara da ashirin suka jikkata, inda adadin ya haura na 2015 da kashi uku. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China