in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Namibia zai ba da kashi 20 cikin dari na albashinsa ga yara matalauta
2015-10-19 11:10:23 cri

Shugaban kasar Namibia Hage Geingop ya dauki niyyar ba da kashi 20 cikin 100 na albashinsa ga wata gidauniyar kudin karatu domin yaran da iyalansu suke fama da talauci.

Shugaban kasar ya yi wannan alkawari a ranar Asabar a yayin da yake wani jawabi a gaban magoya bayan jam'iyyarsa ta Swapo mai mulki, a birnin Windhoek, inda ya kaddamar da kamfen yakin neman zabe na jam'iyyar domin zabukan kananan hukumomi na jahohi da aka tsai da shiryawa a cikin wata mai zuwa.

A shirye nike in kebe kashi 20 cikin 100 na albashina domin kafa wata gidauniyar kudin karatu domin yara mataulata, in ji Hage Geingop a gaban daruruwan magoya bayansa da suka taro a zauren taruka na Katutura.

Albashin shugaba Geinob ya kusan kai dalar Namibia miliyan biyu, kimanin dalar Amurka dubu 76.

Gwamnatin Namibia ta dauki matakin kawar da talauci a matsayin babban aikinta, tare da kafa ma'aikatar kawar da talauci da jin dadin al'umma. Kimanin kashi 28.7 cikin 100 na al'ummar Namibia ke rayuwa cikin talauci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China