in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Assad ya fadada shirin afuwa ga 'yan tawaye da suka yarda su ajiye makamai
2017-02-06 09:35:46 cri

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria, ya amince da fadada shirin gwamnatin sa, na yiwa 'yan tawayen da suka amince su ajiye makamansu afuwa. An dai kaddamar da wannan shiri ne cikin shekarar da ta gabata, inda a wannan karo kuma aka tsawaita aikinsa zuwa watan Yunin wannan shekara.

Shirin ya tanaji cikakkiyar afuwa ga wadanda suka yi fito na fito da gwamnatin kasar, da wadanda suka ci amanar kasar, da masu garkuwa da jami'ai, muddin dai sun amince su ajiye makamansu cikin wannan wa'adin. Wannan ne dai karo na biyu da aka tsawaita wa'adin wannan shiri na afuwa a Syria.

Gwamnatin shugaba Assad na kallon shirin na afuwa, a matsayin wata dama ta musamman, wadda 'yan tawayen kasar ke da ita, ta ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya.

Hakan kuma na zuwa ne yayin da mahukuntan na Syria, da tsagin 'yan tawayen kasar ke shirin bude sabbin shawarwari nan gaba cikin wannan wata a birnin Geneva, kusan wata guda tun bayan da sassan biyu suka amince da shirin tsagaita bude wuta, wanda kasashen Turkiyya da Rasha ke marawa baya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China