in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta baiwa Syria tallafin jin kai na dala miliyan 16
2017-02-06 10:32:59 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin a Syria, da hadin gwiwar ofishin gudanar da tsare tsare da hadin gwiwar kasa da kasa na Syria ICC, sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi biyu, wadanda za su share fagen gabatar da tallafi ga Syria, wanda kimar sa ta kai dalar Amurka miliyan 16.

Jakadan Sin a Syria Qi Qianjin, da shugaban ofishin ICC Imad Sabuni ne suka sanya hannu kan yarjeniyoyin. Ana sa ran karkashin hakan, Sin za ta ba da tallafin jin kai karo biyu ga mabukata a kasar ta Syria. Za kuma a fara wannan aiki ba tare da wani bata lokaci ba, kamar dai yadda Mr. Qi ya ambata.

Yayin zaman sanya hannu kan wadannan yarjeniyoyi da aka yi a birnin Damascus, Mr. Qi ya bayyana farin cikinsa game da tabbatar wannan kuduri mai muhimmanci, yana mai cewa, Sin ta taimaka, kuma za ta ci gaba da tallafawa Syria a wannan mawuyacin hali da take ciki.

Ambasada Qi ya ce, ko shakka babu, an cimma nasarori da dama a yunkurin da ake yi na sake dawo da zaman lafiya a yankuna kasar, ciki hadda nasarar sake kwato birnin Aleppo daga ikon 'yan tawaye.

Kaza lika Mr. Qi ya jinjinawa yunkurin siyasa da ake dauka, wajen warware matsalar tsaro a Syria, ciki hadda tattaunawar da sassan masu ruwa da tsaki suka gudanar a birnin Astana, yana mai fatan za a cimma karin nasarori a taron dake tafe nan gaba a birnin Geneva, inda ake sa ran kara fadada samar da damammaki na siyasa, kari kan nasarorin da aka cimma a taron birnin Astana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China