in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya kaddamar da katafariyar kotu da kamfanin Sin ya gina
2015-10-10 10:14:54 cri

A ranar Juma'ar nan shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, ya tabbatar wa al'ummar kasar aniyarsa ta yaki da rashawa.

Shugaba Mahama ya tabbatar da hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren gini na ma'aikatar shari'a da ya lakume miliyoyin daloli, shugaban ya jaddada cewar, gwamnatinsa za ta mai da hankali wajen inganta ayyukan hukumomin kasar, musamman ma batun yaki da aikata rashawa a kasar.

Katafaren ginin mai dakuna 42, wani kamfanin kasar Sin wato China State Hualong Construction, Ghana Limited ne ya gudanar da aikin ginin.

Babban jojin kasar Georgina Wood, ya ce, yanzu bangaren shari'ar kasar yana kokarin tunkarar yaki da aikata rashawa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China