in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da tallafin alluran rigakafin cutar Malariya ga Ghana
2015-11-18 09:46:40 cri

Gwamnatin kasar Sin ta ba da gudumowar alluran rigakafin cutar Malariya kimanin dubu 600 ga kasar Ghana.

Jakadan kasar Sin a Ghana Sun Baohong, da ministan lafiya na kasar Ghana Alex Segbefia, ne suka halarci bikin mika alluran rigakafin a ranar Talatar nan.

An kiyasta kudin alluran rigakafin kimanin dalar Amurka miliyan 1 da dubu 300, kuma wani kamfanin kasar Sin ne ya samar da alluran.

Kasar Sin ta fara ba da tallafin alluran rigakafin cutar Malariya ga kasar Ghana ne tun a shekarar 2006, a cewar jakadan na Sin, baya ga tallafin magungunan, kasar Sin ta giggina asibitoci da ba da horo na musamman ga jami'an lafiya na kasar Ghana a lokuta dabam dabam.

Mista Sun, ya kara da cewar, dandalin da ake sa ran gudanarwa kan hadin gwiwwar Sin da Afrika a birnin Johannesburg a watan Disamba, zai ba da dama wajen sake karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangaren, Segbefia, ya yaba wa gwamnatin kasar Sin wajen tallafawa fannin kiwon lafiyar kasar ta Ghana, sannan ya bayyana kasar Sin a matsayin kasar da ta yi fice wajen ciyar da fannin lafiya gaba a duniya.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China