in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitocin Sin sun gudanar da aikin tiyatar zuciya a Ghana kyauta
2015-12-11 10:02:46 cri

Tawagar kwararrun likitocin kasar Sin a fannin cutukan zuciya, sun gudanar da aikin tiyatar zuciya ga marasa lafiya kimanin 10 a asibitin koyarwa na Komfo Anokye dake birnin Kumasi a kasar Ghana.

Tawagar kwararrun mai mutane 10 na cibiyar nazarin cutukan zuciya ta Guangdong, sun gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar takwarorin su na kasar Ghana.

Jami'an, sun gudanar da aikin tiyatar ne ga mutane da cutar ta yiwa mummunar illa, ta yadda wasu daga cikin su ba sa ma iya gudanar da al'amurran yau da kullum.

Wani kwarrare na asibitin koyarwar Ghana Dr Isaac Kofi Owusu, ya ce, an samu gagarumar nasara a aikin tiyatar, sannan tawagar jami'an suna matukar farin ciki da kyakkyawan sakamakon da aka samu.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran kasar Sin a ranar Larabar nan Dr Isaac, ya ce, tawagar kwararrun da marasa lafiyan da aka yiwa aikin, dukkanin suna cikin yanayi na farin cikin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China