in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Syria sun isa wajen garin Ain Fijeh karkashin kariyar muggan makamai
2017-01-19 10:50:11 cri

A wani yunkuri na kwato yankin tare da dawo da tura ruwa birnin Damascus, kafafen yada labaran sojin Syria, sun ce dakarun kasar sun isa wajen garin Ain Fijeh, inda nan ne matattarar ruwa da ake turawa birnin Damascus, karkashin kariyar makaman roka.

Sojojin dake samun goyon bayan mayakan Hezbollah na Lebanon, sun kutsa wajen garin Ain Fijeh dake arewa maso yammacin Damascus, karkashin kariyar manyan makaman roka da aka saita kan maboyar 'yan tawaye a yankin da idon ruwan yake.

Manufar kutsen sojojin ita ce, kwato idon ruwan tare da dawo da aikin tura ruwa Damascus, wanda ke fama da matsalar karancin ruwa tun a ranar 22 ga watan Disamban da ya gabata, lokacin da idon ruwan ya daina aiki sanadiyyar kazantar rikici.

An ce, baya ga rikicin da ya barke a jiya Laraba, tsakanin sojojin da 'yan tawaye, an kai gomman hare-hare ta sama.

Dukkan bangarorin dake rikici na nuna yatsa ga juna game da wanda ke da alhakin katse hanyar ruwan, inda gwamnati ke zargin 'yan tawayen Nusra Front dake da alaka da Al-Qaida da katse ruwan da gangan, domin amfani da shi a matsayin makamin da zai tilastawa gwamnati biya mata bukatunta, yayin da 'yan tawayen kuma, ke dora laifin a kan hare-haren dakarun gwamnati. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China