in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a daukacin fadin Syria
2016-12-30 09:20:18 cri

Daukacin sassa a kasar Syria sun rungumi yarjejeniyar tsagaita bude wuta, wadda aka cimma tsakanin manyan kasashe masu shiga tsakani wato Turkiyya da Rasha, a wani mataki na share turbar sulhunta rikicin siyasar dake addabar kasar.

Rundunar sojin kasar ta Syria dai ta ce, an fara aiwatar da yarjejeniyar ne tun daga tsakar daren jiya Alhamis. Sabanin makamantan wannan yarjejeniya da aka cimma a baya, a wannan karo dukkanin kungiyoyin 'yan adawar kasar, ciki hadda "Nusra Front" mai alaka da Al-Qaida, da ma rashen kungiyar IS dake kasar sun amince da ita.

Da yake karin haske game da wannan nasara da aka cimma, ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid al-Moallem, ya ce dakatar da bude wuta na wannan karo, zai ba da dama ta kafa wani ginshiki na warware danbarwar siyasar kasar da aka dade ana fama da ita.

Al-Moallem ya ce, Rasha ta ba da tabbacin goyon bayan wannan mataki, kasancewar ta babbar abokiyar hulda ga Syria, a fannin yaki da ayyukan ta'addanci, ta kuma alkawarta daukar matakan da suka dace kan duk wanda ya yi kunkurin yiwa wannan kuduri kafar ungulu.

Kaza lika a cewar ministan, sabon matakin dakatar da wutar, ya zo a gabar da dakarun sojin gwamnatin kasar suka amshe iko da muhimmin birnin nan na Aleppo dake arewacin kasar, wanda hakan babbar nasara ce ga gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Shugaba Assad dai ya alkawarta martaba wannan yarjejeniya, yayin wata zantawa da ya yi ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China