in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi na'am da yunkurin warware matsalar Somalia bisa doka
2014-12-11 10:21:48 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana gamsuwa ga matakan da ake dauka na warware takaddamar siyasar da ta kunno kai tsakanin firaminista, da shugaban kasar Somaliya ta hanyar biyayya ga dokokin kasar.

Wata sanarwa da kwamitin tsaron ya fitar a jiya Laraba, ta nuna amicewar kwamitin da matakin da majalissar dokokin kasar ta dauka, na kada kuri'ar yanke kauna ga firaministan kasar ta Somaliya, tare da sake jaddada goyon bayan mambobin kwamitin ga manufar warware rikicin siyasar kasar ta hanyar lumana.

A daya hannun kuma, mambobin kwamitin tsaron sun bayyana matukar muhimmancin gaggauta sake daidaitar al'amura a kasar, musamman ma a wannnan lokaci da ake ci gaba da yaki da dakarun kungiyar Al Shabaab, baya ga bukatar dorawa, kan ci gaban da aka samu a fannin aiwatar da sabbin manufofin ci gaban siyasar kasar.

Kaza lika sanarwar ta ja hankalin bangarorin siyasar kasar ta Somaliya, da su mai da hankali kwarai ga manyan manufofin ci gaba, da suka hada da aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin kundin mulkin kasar, tare da kafa dokokin da za su samar da managarcin tsarin zabe. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China