in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da UNHCR za su mayar da 'yan gudun hijirar Somalia dubu 500 zuwa kasarsu
2015-11-04 10:36:01 cri

Kasar Kenya ta ce tana gudanar da aiki na hadin gwiwa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR domin samun nasarar mayar da 'yan gudun hijirar Somalia dubu 500 zuwa kasarsu, wadanda yanzu haka ke zaune a wasu sansanonin 'yan gudun hijira 5 dake Dadaad a kasar Kenya.

Babban sakataren gudanarwar hukumar Joseph Nkaisery, ya ce, gwamnatin Kenya na ci gaba da aiwatar da tsare tsaren da suka dace, wadanda suka hada da tura dakarunta kasar Somalia domin aiki da tawagar wanzar da zaman lafiya ta AMISOM, sannan za'a sake giggina asibitoci da makarantu da samar da ruwan sha kafin sake mayar da 'yan gudun hijirar kasarsu.

Nkaisery, ya ce, kafin a mayar da 'yan gudun hijirar, sai an tabbatar da zaman lafiya ya kankama a Somalia, a don haka ne ma Kenya ta tura dakarun ta kasar, domin gudanar da shirin samar da tsaro a kasar.

Hukumomin kasar ta Kenya sun ce, a shekaru 2 da suka gabata, an mayar da 'yan gudun hijiara dubu 45 gidajensu daga sansanin 'yan gudun hijiarar na Dadaad, kuma ana sa ran a nan gaba wasu karin 'yan gudun hijirar za su koma gidajensu lami lafiya ba tare da fuskantar tashin hankali ba.

Za'a tallafawa 'yan gudun hijirar da motocin da za su kwashe su zuwa garuruwansu na asali, da suka hada da Kismayo da Mogadishu da Baidoa da kuma Luuq dake shiyyar kudanci da tsakiyar Somalia.

Tuni dai aka tallafawa 'yan gudun hijirar da kudade, da kayan abinci, da kayan shimfida, da fitila mai amfani da hasken rana, da kayan dafa abinci domin su sake sabuwar rayuwa.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta ce, sama da 'yan gudun hijirar dubu 26 wadanda suka tsere zuwa Yemen a sakamakon rikicin, sun koma gidajensu, kuma mafi yawansu sun fito ne daga Mogadishu.

Kasar Kenya ta bayyana cewar, ci gaba da zaman 'yan gudun hijirar wata barazana ce gare ta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China