in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi ministan harkokin wajen kasar Chadi a matsayin sabon shugaban AU
2017-01-31 12:13:47 cri
A jiya Litinin ne taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 28 ya zabi ministan harkokin wajen kasar Chadi Moussa Faki Mahamat a matsayin sabon shugaban hukumar zartarwar kungiyar bisa wa'adin shekaru hudu.

Mahamat ya yi nasarar lashe wannan mukami ne bayan da ya kayar da abokan takararsa hudu da suka fafata a neman wannan mukami. Wato ministocin harkokin wajen kasashen Botsawana Pelonomi Venson-Moitoi, na Equatorial Guinea Agapito Mba Mokuy, da ta Kenya Amina Mohammed da na Senegal Bathily Abduolaye kana manzon musamman na MDD mai kula da Afirka ta tsakiya.

A karon farko 'yan takarar guda biyar sai da suka gabatar da wata muhawara ta talabijin a watan Disamban da ya gabata a hedkwatar kungiyar ta AU da ke birnin Addis Ababan kasar Habasha gabanin wannan zabe.

Yanzu dai Mahamat zai maye gurbin Madam Nkosazana Dlimini Zuma 'yar kasar Afirka ta kudu, kana mace ta farko da aka zaba a wannan mukami a shekarar 2012.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China