in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Antonio Guterres ya yi alkawarin aiki tare da kungiyar AU
2017-01-31 12:59:45 cri

Sabon babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana aniyar sa, ta aiki kafada da kafada da kungiyar hadin kan Afirka ta AU, yana mai cewa kungiyar na aiki tukuru wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar ta Afirka.

Mr. Guterres wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, gaban mahalarta taron shugabannin kungiyar ta AU karo na 28 dake gudana a Addis Ababan kasar Habasha, ya ce MDD za ta hada gwiwa da AU wajen cimma muradun nahiyar Afirka, wadanda suka hada da wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Ya ce yana farin cikin ganin yadda nahiyar ke tura tawagogin ta, domin aiki cikin rundunonin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa masu yawa, da ma karbar 'yan gudun hijira da nahiyar ke yi.

A daya bangaren kuma, babban magatakardar MDDr ya ce wasu kasashen nahiyar ta Afirka, na sahun gaba wajen samun ci gaba cikin sauri a duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China