in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi Quartey a matsayin mataimakin shugaban AU
2017-01-31 12:25:20 cri
A wani labarin kuma, a jiyan ne a taron kolin kungiyar AU da ke gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya zabi jami'in diflomasiya dan kasar Ghana Thomas Quartey a matsayin mataimakin shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU,

Kafin zabarsa a wannan mukami Quartey ya shafe shekaru 35 yana aiki a matsayin ma'aikacin diflomasiya, ya kuma yi aiki a matsayin sakataren tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama, mukamin da ya rike har zuwa ranar 7 ga watan Janairun wannan shekara.

Bugu da kari, Quartey ya yi aiki a ofisoshin jakadancin kasar Ghana dake kasashen Cuba, Brussels, baya ga zama wakilin din-din-din na kasar ta Ghana a MDD.

Sauran mukaman da ya rike sun hada da darektan fasfo da kuma mataimakin jakadan ofishin jakadancin Ghana dake Burtaniya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China