Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da iznin hana musulmi daga kasashe bakwai shiga kasar.
Wata majiya daga filin jiragen saman kasar ta Masar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa,wannan mataki wani bangare ne na bukatar da mahukuntan kasar Amurka suka gabatarwa kamfanin jiragen kasar Masar, sai sun gabatarwa bangaren Amurkar sunayen fasinjojin da ke son shiga Amurka kafin daga bisani Amurkar ta yanke shawara a kai, kuma wannan mataki ya shafi dukkan kasashen duniya.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, an haramtawa iyalan kasar ta Iraki da 'yayansu guda biyu tashi daga Masar zuwa kasar ta Amurkan ne saboda, kasar ta Iraki tana cikin jerin sunayen kasashen da Amurka ta haramtawa 'yan kasarta shiga kasar Amurka.
A ranar Jumma'a ce shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannun kan dokar shugaba, wadda ta dakatar da baiwa musulmi daga kasasahen Syria, Iraki,Yemen,Libya,Sudan, Somaliya da Iran iznin shiga kasar.(Ibrahim)