in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin ban ya halaka masu gadi a Somaliya
2017-01-05 11:04:40 cri
Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, wani bam da aka dana a cikin wata mota a kusa da ginin shirin raya kasashe na MDD (UNDP) da ke birnin Mogadishu, ya jikkata masu gadi 4 dake aiki a hukumar. Sai dai kuma hukumar ta UNDP ta tabbatar da cewa, harin bai shafi ma'aikatan da ke cikin wannan gini ba.

Dakarun tsaron Somaliya dai sun yi nasarar damke mayakan kungiyar Al-shabaab wadanda suka sanar da daukar alhakin kai harin da ake niyyar kaiwa ma'aikatan hukumar ta UNDP.

Harin na jiya Laraba na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu tagwayen hare-haren ban da aka dana a cikin wata mota a kusa da sansanin MDD dake birnin na Mogadishu wadanda suka halaka mutane a kalla 2 .(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China