Gwamnatin Nigeriya da ke yammacin Afrika a ranar Laraban nan ta tabbatar da barkewar cutar murar tsuntsaye a jihohi 11.
Ministan ayyukan gona da raya karkara Akinwumi Adesina ya tabbatar da hakan a wata ganawa tare da kwamishinonin ayyukan gona na jihohi ta gaggawa a kan cutar murar tsuntsayen a Abuja babban birnin kasar.
Ya sanar da cewar, gwamnatin ta amince da kudin da za'a biya manoman da wannan cuta ta shafa diyya, don haka ya umurci cewa, a biya diyyar cikin awanni 72.
Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, jihohin da wannan cutar murar tsuntsayen ta shafa suka hada da Kano, Ikko, Ogun, Rivers, Delta, Edo, Filato, Gombe, Imo, Oyo, da Jigawa.
Ya ce, diyyar ta gonaki 39 a cikin jihohi 9 ne wadanda aka kawar da kiwon da hakan ya shafa domin dakile yaduwar ta. (Fatimah)