Gwamnatin kasar Benin ta hana shigo, rarrabawa da jigilar tsuntsaye, nau'in kayayyakin abincin da aka sarrafa da kaji, 'yan tsaki, kwai, abincin dabbobi da duk wasu sauran kayayyakin da aka hada da kaji ko kwai da ake fito da su daga Najeriya, bisa matakan yin rigakafi da duk wata yaduwar cutar murar tsuntsaye, in ji wata sanarwa ta ma'aikatar noma da kiwo ta kasar Benin. A cewar wannan sanarwa da aka fitar a ranar Talata a birnin Cotonou, likitocin dabbobin Najeriya, ta hanyar kungiyar kiwon lafiyar dabbobi ta kasa da kasa, sun sanar da cewa, an sake samun bullowar cutar murar tsuntsaye mai hadari sosai a arewacin kasar a Kano da kuma kudancin kasar a Lagos. (Maman Ada)