in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 605 daga hannun mayakan Boko Haram
2016-12-15 09:41:28 cri

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta samu nasarar ceto wasu mutane da yawan su ya kai 605 daga hannun mayakan kungiyar nan ta Boko Haram, bayan wasu simame da jami'an ta suka kaddamar a dajin Sambisa dake jihar Borno.

Kwamandan tawagar runduna mai yaki da kungiyar Boko Haram, wadda ake yiwa lakabi da "Operation Lafiya Dole" Lucky Irabor, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno.

Mr. Irabor ya ce, tsakanin ranekun 7 zuwa 14 ga watan Disambar nan, dakarun rundunar sun ceto maza 69, da mata 180, da yara maza 227 da kuma yara mata 129. Kaza lika a cewar sa wasu daga wadanda aka ceto din na hannun rundunar ana kuma ci gaba da tantance su.

Jami'in ya kara da cewa, tuni dakarun sojin kasar suka kakkabe mayakan Boko Haram daga wurare da dama, aka kuma saki wasu daga wadanda kungiyar ke garkuwa da su, yayin da kuma da dama daga mayakan kungiyar suka rasa rayukan su yayin musayar wuta da sojojin Najeriyar.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai ya kasance tungar mayakan kungiyar ta Boko Haram. Sai dai a baya bayan nan sojojin kasar na kara matsa kaimi wajen ganin bayan kungiyar, inda suke ci gaba da kaddamar da farmaki a sassan daban daban na yankin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China