A jiya Litinin ne, rundunar 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta tabbatar da aukuwar hare-haren kunar bakin wake uku a Maiduguri, babban birnin jihar, da kuma wani tsohon sansanin mayakan kungiyar Boko Haram.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Victor Esuku, ya ce hare-haren da aka kai ranar Lahadi, sun yi sanadiyyar mutuwar wasu fararen hula biyu da wani dan banga.
Victor Esuku ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua cewa, 'yan kunar bakin waken sun yi kokarin shiga cikin birnin Maiduguri ta yankunan Garki Muna da Kaleri dake jihar.
Ya ce, 'yan kunar bakin wake maza guda uku, sun tarwatsa kansu a kusa da shingen binciken soji dake Garki Muna, yayin da biyu mata kuma suka rasa rayukansu a Kaleri.
A watan da ya gabata ne, jami'an tsaron Nijeriya dake yankin arewa maso gabashin kasar, suka kai farmaki kan 'yayan kungiyar Boko Haram, inda suka fatattake su daga dajin Sambisa. ( Fa'iza Mustapha)