Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna takaici game da harin ta'addanci da aka kai a jami'ar Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin kasar da safiyar jiya Litinin.
Hukumomin 'yan sanda a jihar Borno sun ce, 'dan kunar bakin waken ya kaddamar da harin ne a jami'ar Maiduguri a jihar Borno, inda ya hallaka a kalla mutane 5, kana wasu mutanen 15 suka samu raunuka.
Dan kunar bakin waken 'dan shekaru 7 ya tada bam din dake jikinsa ne a wani masallaci dake rukunin gidajen manyan ma'aikatan jami'ar Maiduguri. Bom na farko ya tashi ne yayin da 'dan sandan dake aiki a wajen ya harbo shi a daidai lokacin da maharin ke kokarin tsallakawa ta kan wani shinge daga cikin hanyoyin shiga jami'ar.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a Abuja, shugaba Buhari ya nuna juyayi tare da mika sakon ta'aziyya ga ma'aikatan jami'ar da iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Da yake yin Allah wadai da harin, shugaban na Najeriya ya bukaci al'ummar kasar su taimaka wajen yakar ta'addanci a kasar.
Buhari ya ce, wadanda ke shirya hare haren ba su fahimci addinin musulunci ba, kana ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da murkushe duk wata barazanar ayyukan ta'addanci dake haifar da illa ga zaman lafiyar al'ummar kasar.(Ahmad Fagam)