Majalisar dokokin Nijeriya a jiya Laraba, ta ce za ta yi bincike kan harin da jirgin yakin soji ya kai sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno, da nufin tantance ko hakan ya yi daidai da dokar luguden wuta ta sama, da kuma dokar ba da agajin jin kai ta kasa da kasa.
Harin da aka kai a ranar Talata da ta gabata, wanda tuni rundunar sojin ta ayyana shi a matsayin kuskure, ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla hamsin da biyu yayin da ya jikkata wasu dari da ashirin.
Wani 'dan majalisar dokokin kasar Muhammad Zoro, ya ce majalisar na kuma duba yiyuwar gabatar da wani kuduri, da zai tantance irin taimako da wadanda suka tsallake rijiya da baya ke bukata, da kuma yadda ake kula da lafiyar wadanda suka jikkata.
Tuni shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana matukar damuwa da jimami game da al'amarin, yana mai cewa, hadarin ya auku ne a lokacin da sojojin suka shiga wani mataki na karshe, na murkushe ragowar 'yan tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.
A yanzu dai, rundunar sojin Nijeriya, ta matse kaimi wajen kai hare-hare ta sama da kasa a yankin arewa maso gabashin kasar zuwa yankunan dake makwaftaka da kasashen Nijer da Chadi.( Fa'iza Mustapha )