in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya gana ta wayar tarho da zababben shugaban Gambia game da batun mika mulki cikin ruwan sanyi
2016-12-30 09:28:04 cri

Jiya Alhamis 29 ga wata, sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya gana ta wayar Adama Barrow, zababben shugaban kasar Gambia, inda ya ce, MDD ta kuduri niyyar mara baya ga batun mika mulki cikin ruwan sanyi, kuma a kan lokaci a kasar.

A cewar ofishin kakakin MDD, Ban Ki-moon, ya kuma taya Adama Barrow murnar lashe zabe da ya yi, yana mai bukatarsa da ya yi kira ga magoya bayansa su kauracewa tada fitina.

Adama Barrow dai ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 1 ga watan da muke ciki, inda shugaban kasar mai ci Yahya Jammeh ya amince da kayen da ya sha. Sai dai, kwanaki kalilan bayan amincewar ta sa ne kuma, ya sake fitowa ya yi fatali da sakamakon zaben.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne wa'adin shugabancin Yahya Jammeh zai kare.

Domin tabbatar da mika mulkin cikin kwanciyar hankali, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS, ta yanke shawarar tura dakaru domin tabbatar da tsaron zababben shugaban da shugabannin siyasa da daukacin al'ummar kasar.

Ban ki-moon ya ce, MDD na maraba da matakin da ECOWAS din ta dauka, inda ya ce, a shirye MDD take, ta mara baya ga shugabancin Adama Barrow a kokarin inganta tsarin demokradiyya, da samar da ci gaba mai dorewa a kasar Gambia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China