in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan kunar bakin wake 2 sun mutu a Najeriya
2016-12-20 09:43:15 cri

Wata majiya daga hukumar 'yan sanda a Najeriya ta bayyana cewa, wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake sun mutu bayan da boma boman dake jikinsu ya tashi da su a lokacin da suka yi yunkurin kutsawa birnin Maiduguri, fadar mulkin jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar da niyyar kaddamar da hare hare.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jahar Victor Isuku, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan kunar bakin waken sun gamu da cikas ne a lokacin da jami'an tsaro ke ci gaba da tsananta bincike a wasu kauyuka dake wajen birnin Maiduguri.

A cewar Isuku, guda daga cikin maharan ne ta tada boma boman dake daure a jikinta, inda nan take ta hallaka tare da abokiyar harinta.

Kakakin hukumar 'yan sanda ya kara da cewa, wasu mazauna yanki su 3 sun samu raunuka a sakamakon faruwar lamarin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China