A jiya Laraba kasar Algeriya ta bukaci al'ummar kasar Mali da ba sa ga maciji da juna da su rungumi hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a kasar, kana ta yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kaddamar a arewacin birnin Gao.
"Kasar Algeriya ta yi kakkausar suka game da harin ta'addancin da aka kaddamar a yau a birnin Gao", kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Malin Abdelaziz Benali ya sanar wanda kamfanin dillancin labaran APS na kasar ya sanar.
Ya kara da cewa, Algeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da hada kai da mahukuntan kasar Mali da kasashen duniya, wajen daukar matakai da za su tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Mali.
Dan kunar bakin waken ya yi yunkurin kaddamar da harin ne a sansanin sojojin kasar dake birnin Gao, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 50, da kuma jikkata mutane 60.(Ahmad Fagam)