in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya na fatan ganin sulhu tsakanin 'yan tawayen Mali da gwamnatin kasar
2014-07-18 10:43:40 cri

Ministan harkokin wajen kasar Algeriya Ramtane Lamamra ya ce, kasarsa na fatan za'a samu daidaito a tsakanin gwamnatin kasar Mali da 'yan tawayen Tuareg na arewacin kasar, wadanda yanzu haka suke zaman tattaunawa na sulhu a Algiers, babban birnin kasar Algeriya tun ranar Laraba domin cimma daidaito kafin karshen watan nan na Azumin Ramadan.

Mr. Ramtane Lamamra wanda ya sanar da wannan fata, ya ce, kafin a fara zaman sulhu na ranar Laraba, gwamnatin Mali da 'yan tawaye na Tuareg sun cimma yarjejeniyar musanyar fursunoni a tsakaninsu wadda Algeriya ta zama shaida a wannan zama, abin da ya ba da kwarin gwiwwa ga tattaunawar da ake yi a yanzu.

Tun daga ranar Laraba, Algeriya ta dauki nauyin zaman sulhun a tsakanin bangarori biyu a karo na farko da fatan za'a cimma daidaito a siyasance da zai samar da tsaro a arewacin Malin dake fuskantar rikici. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China