Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da gagarumar rawar da Algeria ta taka a shirin samar da zaman lumana a kasar Mali.
Magatakardan MDD ya bayyana hakan a yayin da ya gana da ministan harkokin waje na kasar Algeria Ramtane Lamamra, wanda ke birnin New York a halin yanzu domin halartar taron kolin MDD a kan canjin yanayi.
Ban Ki-moon ya kuma yi kira a kan daukacin wadanda ke kokarin wanzar da zaman lafiya a Mali, da su ci gaba da hada karfinsu wuri guda da zimmar tallafawa tsare-tsare na siyasa na kasar ta Mali domin kaiwa ga nasara.
A halin da ake ciki kasar ta Mali na aiwatar da wani shiri na maido da tsarin damokradiyya, tare da taimakon MDD da kuma kungiyoyi na yankuna wanda suka hada da kungiyar tarayyar hadin kan Afrika da kuma kungiyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afrika. (Suwaiba)