An kashe a kalla mutane 17 da ake zargi masu tsattsauran ra'ayi ne, a wadansu hare-haren tabbatar da tsaro da aka kai birnin Rafah na gundumar Sinai dake arewacin kasar Masar.
Wata majiya ta tsaro ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, dakarun gwamnatin Masar sun kashe 'yan tsagera 12, wadanda aka yi amanna a bisa cewar, 'yayan kungiyar musulmi ce ta Ansar Bayt al-Maqdis, mai alaka da kungiyar al-Qaida.
Majiyar ta kara da cewar, sojojin Masar sun kuma lalata motocion 'yan tsageran, tare da kame 3 daga cikin 'yan tsageran, a yayin da suke kokari su dasa bama-bamai a wadansu wurare.
Wannan gagarumin kamfe na hare-haren tabbatar da tsaro, da sojojin na Masar suka kai da hadin gwiwar 'yan sandan kasar a kan kungiyoyin 'yan tsagera, dake yankin Sinai, ya zo daidai da shekara guda cif, bayan wancakalar da gwamnatin islama ta tsohon shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi. (Suwaiba)