in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi allahwadai da kara tsawaita takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2014-10-27 09:54:20 cri

Kasar Sudan ta yi allahwadai da shawarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yanke na kara tsawaita wa'adin takunkumin tattalin arziki na Afirka da Amurka ta kakaba mata.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a ranar Lahadi, inda kasar ta Sudan ta yi allahwadai da wannan mataki, kana ta yi watsi da dalilan da aka yi amfani da su wajen kara tsawaita wannan takunkumi.

Sanarwar ta ce, kara tsawaita wannan takunkumi ba zai hana gwamnatin Sudan kara kokarin da take na tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a kasar ba. Kana ta zargi kasar Amurka da tsoma baki cikin harkokinta.

A nasa bangare, shugaba Obama na Amurka ya ce, ya dauki wannan mataki ne, saboda ganin yadda matakai da manufofin gwamnatin Sudan ke ci gaba da haifar da barazana ga harkokin tsaron cikin gida da manufofin kasashen waje na Amurka.

A ranar Jumma'a ne shugaba Obama ya kara tsawaita wa'adin shekara guda kan takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar ta Sudan tun a shekara 1997. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China