in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kara wa'adin tsagaida bude wuta da watanni 6
2017-01-16 09:48:48 cri

A jiya Lahadi ne majalisar ministocin kasar Sudan ta kara wa'adin tsagaida bude wuta da sojojin gwamnatin kasar suka cimma da bangaren 'yan tawayen kasar da watanni shida.

An cimma wannan shawara ce yayin wani zama na musamman da shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya jagaronta.

A ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2016 ne dai shugaba al-Bashir ya sanar da kara wa'adin tsagaita buden da wata guda a dukkan yankunan kasar ta Sudan da ake gwabza fada, ciki har da yankunan Darfur, kudancin Kordofan da Blue Nile.

Tun a shekarar 2011, gwamnatin kasar ta Sudan ta ke fada da dakarun da ke fafutukar kwatar 'yancin Sudan, bangaren arewaci a jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile, duk da tattaunawar zaman lafiya da bangarorin biyu suka yi har sau goma a birnin Addis Ababan kasar Habasha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China