in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SPLM ta Sudan ta zargi dakarun gwamnati da take yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2017-01-10 09:07:44 cri

Bangaren kungiyar 'yan tawayen SPLM dake arewacin Sudan, ta zargi dakarun gwamnatin kasar da kai hari wani yanki dake karkashin ikonta..

Kakakin kungiyar SPLM dake arewacin Sudan Arno Taloudy, ya ce a jiya Litinin, 9 ga wata, dakarun jam'iyyar NC sun kai hari shiyyar Blue Nile, inda suka farwa 'yayan kungiyar dake yankin Al-Rum na jihar Blue Nile.

Ya ce, kawo yanzu, ana ci gaba da gwabzawa, al'amarin da ya kira da take shirin tsagaita bude wuta da shugaba Al-Bashir ya sanar.

Sai dai dukkan kokari domin jin ta bakin rundunar sojin kasar game da ikirarin da kungiyar 'yan tawayen ta yi ya ci tura.

A ranar 31 ga watan Disamban da ya gabata ne, shugaban Sudan Omar Al-Bashir, ya sanar da tsawaita shirin tsagaita bude wuta da gwamnati da dukkan 'yan tawayen kasar suka cimma da wata guda, a dukkan yankunan da ake rikici. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China