in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutumin da ya kai hari a gidan rawa a Istambul
2017-01-17 09:55:16 cri

A jiya ne 'yan sanda a birnin Istambul na kasar Turkiya suka yi nasarar cafke mutumin da ya kai hari a jajiberen sabuwar shekara a wani gidan rawa, inda ya halaka mutane 39.

Jaridar Hurriyet da ake wallafawa a kasar a ko wace rana, ta bayyana cewa, 'yan sanda sun kama maharin wanda aka shafe kusan kwanaki 17 ke nan ana nema ruwa a jallo, a gidan wani abokinsa da ke gundumar Esenyurt a yayin wani samame da suka kaddamar.

Rahotanni na cewa, an kuma samu maharin mai suna Abdulgadir Masharipov, 'dan asalin kasar Uzbekistan da wani yaro 'dan shekaru 4.

Kimanin mutane 35 ne dai aka tsare bisa zarginsu da hannu a harin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China