in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin gidan biki a Turkiyya
2016-08-22 11:06:14 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wani gidan biki a kudu maso gabashin kasar Turkiyya, lamarin da ya sabbaba rasuwar mutane a kalla 50, tare da jikkata wasu karin mutanen 94.

Wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, ta rawaito Ban Ki-moon na ce, yana fatan za a kai ga cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su gaban kuliya. Ya kuma sake nanata bukatar kara hadin gwiwa tsakanin shiyyoyi da ma sassan kasa da kasa, domin magance kalubalen ta'addanci da kuma ayyukan masu tsattauran ra'ayi.

Rahotanni sun nuna cewa, wani abun fashewa ne ya tarwatse cikin wani babban zaure dake makare da mutane, yayin da ake tsaka da wani bikin aure a lardin Gaziantep da daren ranar Asabar. An kuma ce, wani matashi ne mai goyon bayan kungiyar IS ya tada abun fashewar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China