Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta sanar a jiya Litinin cewa, wasu mutane da ba'a gano ko su wane ne ba sun kashe mata wani babban jami'inta a jahar Ekiti dake shiyyar kudu maso yammacin kasar.
Mai magana da yawun 'yan sandan jahar Alberto Adeyemi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a garin Ado Ekiti, helkwatar mulkin jahar, ya ce, an tsinci gawar jami'in ne a cikin wata mota a yankin Ajebamidele dake cikin birnin.
Marigayi sufurtanda Idowu Taiwo, an ba da rahoton cewa, a daren Lahadin da ta gabata ne aka yi garkuwa da shi a garin na Ado Ekiti. Kana a jiya Litinin kuma, aka tsinci gawarsa cikin wata mota a birnin na Ado Ekiti.
Sai dai kawo yanzu ba'a gano dalilin da ya sa aka kashe jami'in ba.
Kakakin hukumar 'yan sandan ya fada wa 'yan jaridu cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, amma har yanzu ba'a kama ko da mutum guda ba game da zargin hannu wajen hallaka jami'in.(Ahmad Fagam)