in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mayakan Boko Haram 30 a arewa maso gabashin Najeriya
2016-11-29 09:41:44 cri

Kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 30 ne aka kashe a makon da ya gabata a cikin wani gumurzu tare da rundunar sojojin kasar a jihar Bornon Najeriya dake arewa maso gabashi, in ji wani jami'in wurin a ranar Litinin.

Saeed Salisu Sambo, dake jagorantar yankin Gwoza na jihar Borno, ya bayyana cewa, 'yan ta'addan sun sami wani yakinsu na Waterloo a lokacin da suka yi yunkurin shirya wa wani ayarin jami'an wurin kwantan bauna a lokacin da suke kokarin zuwa Pulka a Maiduguri a ranar Asabar da safe.

Ya bayyana cewa, mayakan na Boko Haram sun tada wata nakiya da su harhada, tare da yin barin wuta a duk tsawon hanyar Bama.

Jihar Borno ta zama wani sansanin kungiyar Boko Haram, inda mayakan na Boko Haram suke kai hari kan rundunar sojojin Najeriya tun tsawon wadannan shekaru shida da suka gabata. Wadannan watanni na baya bayan nan, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wasu ayyukan soja domin murkushe barazanar ta'addanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China