in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an tsaron Sudan sun dakile yunkurin safarar bil adama na mutane 115
2017-01-09 09:51:05 cri

Rundunar wanzar da tsaro ta RSF a kasar Sudan ta sanar a jiya Lahadi cewa, ta kakkabe wani yunkuri na yin safarar bakin haure ba bisa ka'ida ba ta hanyar kungiyoyi masu safarar bil adama a kan iyakokin kasashen Sudan da Masar da Libya.

Dakaraun na RSF, suna aiki ne karkashin hukumar jami'an tsaro ta sirri na kasar Sudan NISS, sun bayyana cewa, sun yi nasarar bankado yunkurin yin safarar bakin hauren ta barauniyar hanya kimanin mutane 115, wadanda mafi yawansu 'yan kasashen Somaliya, da Habasha da kuma Eritrea ne.

Babban kwamandan RSF Muhammad Hamdan Hametti, ya shedawa 'yan jaridu cewa, wadannan bakin hauren, an yi niyyar tsallakawa da su ne zuwa kasar Libya, daga bisani kuma a zarce da su zuwa kasashen Turai.

Ya kara da cewa, za'a damka bakin hauren ga jami'an 'yan sandan kasar Sudan domin su kammala bincike, daga bisani kuma a mayar da su zuwa kasashensu na ainihi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China