in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira a yaki da cin zarafin mata a Sudan ta Kudu
2016-12-08 11:13:46 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi kira a ranar Laraba da a kara karfafa kokari domin yaki da cin zarafin mata da ayyukan fyade Sudan ta Kudu, kasar dake fama da yakin basasa, tare da tabbatar da cewa, dukkan masu aikata wadannan laifuffuka sun dauki laifinsu, kana wadanda lamarin ya shafa, an yi musu adalci da biya musu hakkinsu.

Manzon musammun na kwamitin tarayyar Afrika kan mata, zaman lafiya da tsaro, madam Bineta Diop, ta bayyana a gaban manema labarai a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu cewa, har yanzu matan Sudan da Kudu suna ci gaba da fama da fyade, da rashin tsaro.

Idan har akwai wata niyyar siyasa domin tabbatar da cewa, wadanda suka aikata wadannan laifuffukan cin zarafi, an gurfanar da su gaban kotu, to ina ganin mata za su kanshin makoma mai haske, in ji madam Diop.

Jami'ar na jagorantar wata tawagar kwarraru kan 'yancin mata ta kwamitin AU dake ziyarar aiki ta kwanaki hudu a kasar Sudan ta Kudu, domin jagorantar wani shirin dake shafar maido da mutuncin matan Sudan ta Kudu da suka yi fama da tashe tashen hankali.

Tawagar ta AU za ta gana da manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu, wakilan mata da mutanen da suka kaura domin kimanta halin da ake ciki ta fuskar 'yancin 'dan adam.

Haka kuma, madam Diop ta yi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su samar da damammaki da matsayi ga matan wannan kasa, da yaki mai tsawon shekaru uku ya lalata.

Miliyoyin mutane ne suka mutu yayin da wasu mutane miliyan 2,4 suka kaura daga muhallinsu tun lokacin barkewar yakin basasa a cikin watan Disamban shekarar 2013.

An cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya a cikin watan Agustan shekarar 2015 bisa matsin lambar MDD, wadda ba ta jima ba domin sabbin tashe tashen hankali sun barke tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Salva Kirr da na tsohon mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China