in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya jefa kuri'a a birninsa na asali
2016-12-08 10:44:35 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kada kuri'arsa a ranar Laraba, na zabukan dake gudana, a birninsa na asali na Bole Bamboi dake mazabar Bole dake yankin arewacin kasar.

Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, babban mai adawa da shugaba John Dramani Mahama, ya jefa kuri'arsa a ranar Laraba da safe, a yankin asalinsa na Kyebi dake mazabar Abuajwa ta Kudu, dake shiyyar gabashin kasar.

An bude rumfunan zabe a ranar Laraba da masalin karfe 7 na safe, inda ake sa ran masu zabe miliyan 15 za su zabe shugaban kasarsu da kuma 'yan majalisu 275. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China