in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana: An kafa kwamitin mika mulki
2016-12-13 10:35:27 cri

A Ghana an kafa kwamiti mai mutane 16, domin aikin tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar cikin nasara.

Shugaba mai barin gado John Dramani Mahama, da mai jiran gadon mulkin kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, su ne suka kafa kwamitin bisa tanajin kundin tsarin mulkin kasar.

Hakan dai ya biyo bayan bayyana Akufo-Addo na jami'iyyar adawa ta NPP a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasar na ranar Larabar makon jiya.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da kwamitin, Mr. Akufo-Addo ya bukaci mambobin sa da su hada kai da juna, su kuma gudanar da aiki ta hanyar bin ka'ida. Kwamitin dai zai gudanar da aikin sa har ya zuwa lokacin da za a rantsar da Mr. Akufo- Addo a ranar 7 ga watan Janairun shekara mai kamawa.

Mr. Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasar Ghana ne da kuri'u sama da miliyan 5 da dubu dari 7, kimanin kaso 53.85 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada yayin zaben, yayin da shugaba mai barin gado John Mahama na jam'iyyar NDC ta samu kaso 44.40 bisa dari na yawan kuri'un.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China