Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da wani bincike domin gano wadanda suka hallaka masu aikin hakar ma'adanai su 40 a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.
Shehu Muhammad, shi ne mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Zamfara, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu 'yan bindiga da ake zargin barayin shanu ne suka afkawa mutanen dake aikin hakar ma'adanai a ranar Litinin da ta gabata a kauyen Gidan Ardo dake yankin Bindin na jihar.
Ya ce, 'yan sandan za su gudanar da aiki na hadin gwiwa da sojoji, domin bankado wadanda suka kashe mutanen, ya kara da cewa, har yanzu ba'a kammala tantance adadin mutanen da harin ya rutsa da su ba.
Sai dai, wata majiya daga yankin ta tabbatarwa Xinhua cewa, mutane 40 ne 'yan bindigar suka hallaka a lokacin da suka isa yankin a kan babura, inda suka bude wuta kan masu hakar ma'adanan. A cewar wani jami'i a yankin Ismail Dongo, wasu mutanen da dama sun jikkata a yayin harbe harbe da 'yan bindigar suka kaddamar a yankin.(Ahmad Fagam)