in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta rage takunkumin takaita zirga-zirga da ta kakabawa kungiyoyin jin kai
2016-12-26 09:09:14 cri

Jaridar Tribune ta kasar Sudan ta ruwaito cewa, gwamnatin kasar ta rage takunkumin takaita zirga-zirga da ta sanyawa kungiyoyin ba da agaji dake aiki a kasar, inda ta amince da wasu yin wasu gyare-gyare a tsarin ayyukan nasu.

Kwamishinan kula da ayyukan jin kai na kasar, Ahmed Mohammed Adam, ya ce sake tsarin ya biyo bayan kyautatuwar tsaro da aka samu a jihohin kasar.

Ya ce, sabon tsarin ya kunshi rage takunkumin takaita zirga zirgar jami'in aikin jin kai, inda ya rage bukatar neman izini a yankunan da ake zaman lafiya, yayin da za a ci gaba da neman izini a inda ke da barazanar tsaro.

Ya bayyana fatan cewa, sabbin gyare-gyaren za su ba da damar hada hannu da kungiyoyin wajen kai dauki, domin cimma muradun da aka sanya gaba.

Kungiyoyin ba da agaji na kasashen waje dai na korafin gwamnatin kasar, ta takaitawa jami'ansu zirga-zirga a yankunan da ake rikici.

Inda gwamnatin Sudan din ta ba da dalilai na tsaro a matsayin hujjarta ta hana kungiyoyin isa yankunan dake da hadari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China