in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta janye dakarunta daga tawagar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2016-11-10 09:48:42 cri
Rukunin farko na sojojin kasar Kenya da ya yi aiki cikin tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu ya isa a ranar Laraba a birnin Nairobi bayan umurnin da shugaban kasa Uhuru Kenyatta ya bayar na da su janye. Kasar Kenya ta bayyana a makon da ya gabata cewa za ta janye dakarunta bayan da wani binciken MDD ya zargi tawagar UNIMISS da rashin mayar da martani kan wani hari a wani ginin Otel din dake Juba a yayin tashe tashen hankalin da suka barke a cikin watan Yuli. Haka kuma an dakatar da Laftanal janar Johnson Ondieki daga aikinsa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China