in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiyya za ta tsawaita wa'adin dokar ta baci zuwa karin watanni 3
2017-01-04 10:53:40 cri

Majalisar dokokin kasar Turkiyya a jiya Talata, ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a kasar zuwa karin watanni 3, kamfanin dillancin labarun kasar Dogan ne ya sanar da labarin.

A ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2016 ne Turkiyya ta ayyana kafa dokar ta baci, bayan wani yunkurin juyin mulkin soja a kasar wanda bai samu nasara ba, kasar ta dora alhakin yunkurin juyin mulkin a kan fitaccen malamin addini dan kasar Fethullah Gulen, wanda ke zaune a kasar Amurka.

Karkashin dokar, gwamnatin kasar na da ikon yin gaban kanta ba tare da sahhalewar majalisar ba, wajen zartaswa ko kuma sauya wasu sabbin dokoki da suka shafi 'yancin dan adam a kasar.

Firaministan Turkiyya Binali Yildirim, ya fada a jiya Talata cewa, majalisar dokokin kasar za ta fara yin mahawara kan sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar a makon gobe.

Za a gabatar da daftarin dokokin kasar ne a lokacin babban taron majalisar a ranar 9 ga wannan wata, kuma ana sa ran, zuwa karshen watan ne za'a amince da shi.

Kudurin dokar ya ba da dama ga shugaban kasar ya kasance a matsayin shugaban jam'iyyarsa.

Gwamnatin Turkiyyar ta ce za ta gudanar da aikin jefa kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a game da sauya kundin tsarin mulkin kasar, duk da cewa daftarin dokar ya samu amincewar mafi yawan mambobin majalisar dokokin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China