in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya mika sakon jaje ga takwaransa na Turkiyya game da harin da aka kai Istanbul
2017-01-03 11:14:05 cri
Firaministan Sin Li Keqiang, ya aika da sakon jaje ga Firaministan Turkiyya Binali Yeldrim, game da harin da aka kai Istanbul lokacin bikin sabuwar shekara.

A sakonsa, Li Keqiang, ya jimanta mutuwar mutanen da harin ya rutsa da su, inda ya jajantawa Firaministan da kuma iyalansu, da kuma wadanda suka jikkata.

Da sanyin safiyar ranar Lahadi ne, wani dan bindiga dadi ya kutsa gidan rawa na Reina dake Istanbul, inda ya yi harbin kan mai uwa da wabi, kan daruruwan mutanen da suka taru don bikin shiga sabuwar shekara, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane talatin da tara,yayin da wasu sama da sittin suka jikkata.

Gwamnan Istanbul Vasip Sahin ya bayyana harin a matsayin na ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China