in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaban kasar Sin don taya murnar sabuwar shekara
2016-12-31 19:00:08 cri


A jajibirin sabuwar shekara ta 2017, shugaban kasar Sin mista Xi Jinping, ya yi jawabi ta wasu kafofin watsa labaru na kasar Sin, da suka hada da gidan rediyon kasar Sin CRI, da gidan rediyon CNR, da gidan telabijin na CCTV, da gidan telabijin na CGTN, da kuma shafunan Intanat. Ga cikakken jawabinsa:

Abokai da aminai, jama'a maza da mata:

Yau shekarar 2016 za ta shude, sa'an nan sabuwar shekara na karatowa. A wannan lokaci mai ma'ana, ina so in mika sakon taya murna da fatan alheri ga jama'ar kasar Sin ta kabilu daban daban, da 'yan uwanmu Sinawa dake yakunan musamman na Hongkong da Macau, da na yankin Taiwan, gami da wadanda ke kasashen ketare. Haka kuma ina taya murnar abokanmu da ke kasashe da yankuna daban daban.

Shekarar 2016 tana da muhimmancin da jama'ar kasar Sin ba za su manta da shi ba, ganin yadda a wannan shekara muka samu ci gaba sosai a shirinmu na raya kasa na 13, wanda muke tsara shi duk shekaru biyar biyar. Muna bin sabuwar manufar raya kasa, da gaggauta yunkurin samar da walwala, ta yadda muka sanya tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da zama a kan gaba a duniya. Muna kokarin zurfafa gyare-gyarenmu, da daidaita tsarin da ake bi wajen samar da kayayyaki, da kwaskwarima kan aikin soja, ta yadda muka tabbatar da manyan tsare-tsaren da za a bi domin gudanar da gyare-gyare da fannoni daban daban. Haka zalika, mun sa kaimi ga matakin kula da kasa ta hanyar dokoki, da kokarin gyaran tsarin shari'a, don neman tabbatar da daidaito da adalci ga al'umma. Ban da wannan kuma, mun tsaurara matakan ladabtarwa cikin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kokarin dakile cin hanci da rashawa, ta yadda muka samu damar tsabtace muhallin siyasa, da daidaita ayyukan da suka shafi jam'iyya, harkar gwamnati, da zaman al'umma.

Duk a shekarar 2016, mun kafa wata na'urar binciken sararin samaniya mai taken "Idon kasar Sin". A nasa bangare, kumbo kirar "Wukong" ya yi shekara daya yana shawagi cikin hanyarsa. Haka zalika, mun harbi kumbo na "Mozi", da kumbon "Shenzhou" mai lambar 11, gami da kumbon "Tian Gong" na 2.

A nasu bangare, 'yan wasan kasar Sin sun cimma nasarori da yawa yayin wasannin Olympics da suka gudana a birnin Rio na kasar Brazil. Cikinsu, tawagar 'yan wasa mata ta wasan kwallon raga ta kasar Sin, sun sake lashe lambobin zinariya, bayan wasu shekaru 12 suna ta kokarin nema.

Haka zalika, mun yi kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a ta hanyar gyare-gyare. Ga misali, yanzu manoma masu ci rani sun samu karin damammakin ci gaba da zama cikin birane, haka kuma an kyautata muhallin karatu na yaran dake wasu wuraren da suka fi fama da talauci. Yanzu haka jama'a za su iya samun wani sabon katin shaidar 'yan kasa duk inda suke, kuma mutane da yawa sun samu damar kulla yarjeniyoyi da wasu likitoci, don su rika kula da lafiyar iyalansu, sa'an nan za a nada wani shugaba mai kula da kogi ga duk wani kogin dake nan kasar Sin. Hakika, duk wadannan abubuwa, sun gamsar da mu matuka.

Haka zalika, a shekarar 2016, mun shirya taron koli karon 11 na shugabannin kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, a dab da tabkin Xizi dake birnin Hangzhou na kasar Sin, inda muka nuna basirar Sinawa da dabarar kasar Sin ga kasashen duniya, haka kuma mun daukaka matsayin kasar a idanun mutanen duniya. Ban da wannan kuma, duk a shekarar 2016, muna kokarin aiwatar da shirin " Ziri daya da Hanya daya", tare da bude banki na zuba jari kan aikin gina kayayyakin more rayuwa a nahiyar Asiya. A nan ya kamata mu nuna cewa, Sinawa na tsayawa kan neman ci gaba ta hanyar lumana, da kokarin kare mulkin kai da cikakken yankin kasa, gami da hakkin kasar ta fuskar teku. Don haka, idan wani ya nemi lahanta moriyar kasar Sin a wannan fanni, to, jama'ar kasar sam ba za su yarda da hakan ba!

Duk da haka muna bakin ciki matuka, ganin yadda wasu bala'u daga indallahi sun yi sanadiyyar asarar rayukan jama'a da dukiyoyinsu. Ba za mu manta da sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin da suka sadaukar da rayukansu don tabbatar da zaman lumana a duniya ba, kuma mun yi alkawarin kula da iyalansu yadda ya kamata.

A shekarar 2016, mun shirya babban biki don tunawa da cika shekaru 95 da kafuwar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da zagayowar ranar cika shekaru 80 tun bayan da sojojin karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin suka kammala wata babbar kaurar da suka yi mai taken "Long March" a Turance. Ya kamata mu tuna da mazan jiya da suka samar da gudunmowa ga cigaban al'ummar Sin, da burin da muka sanya a baya, ta yadda za mu san alkiblar da za mu nufa.

Abokai da aminai, jama'a maza da mata:

Waiwaye adon tafiya. Yadda aka waiwayi baya, shi ne domin neman karin ci gaba a ranaku masu zuwa. A shekarar 2017 mai zuwa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta kira taron daukacin wakilanta na sassan daban daban na kasar Sin a karo na 19. A nan mun yi alkawarin ci gaba da kokari a fannonin tabbatar da walwalar al'umma, da zurfafa gyare-gyare, da kula da harkokin kasa ta hanyar dokoki, da tsaurara matakan kula da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Mun san cewa, mutumin da ya shuka shi yake girba. Ba za a samu biyan bukata ba sai da kokarin aiki.

Ban da wannan kuma, ya kamata mu lura da dukkan al'ummar kasarmu, don kar mu bar wani a baya a kokarinmu na neman samun walwala. Cikin shekara daya da ta wuce, an fitar da karin mutane fiye da miliyan 10 daga kangin talauci. A nan ina so in jinjina wa ma'aikata masu kula da aikin kau da talauci, domin na san sun sha wahala matuka wajen kokarin gudanar da ayyukansu. Sai dai, a wannan lokaci na murnar sabuwar shekara, abin da na fi damuwa a kai, shi ne yanayin da matalauta suke ciki. Ina so in san mene ne abin da suke ci? Yaya muhallinsu? Ko za su iya jin dadin biki kamar yadda muke yanzu? Na san wasu mutane suna fama da matsaloli a fannonin neman aikin yi, da ilmantar da yaransu, da ganin likita, da samun gidajen zaune. Kuma na san neman hanyar da za a bi don daidaita wadannan matsaloli shi ne nauyin dake bisa wuyan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatinmu. Kamata ya yi mu ci gaba da kokarin kula da matalauta da wadanda ke da bukata, don sanya karin jama'a su amfana da ci gaban da aka samu ta hanyar gyare-gyare, da kara kyautata zaman rayuwarsu.

Duk abin da ake nema, matukar shugabanni da jama'a suna da buri daya, to, za a cimma burin a karshe. Illa dai jama'armu da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.3 za su yi tsintsiya madaurinki daya, kuma jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dauki matsayin jama'ar kasarmu, ta yi kokari tare da su, to, ina da imani kan samun biyan bukatunmu a karshe.

Abokai da aminai, jama'a maza da mata:

Sinawa sun dade suna da ra'ayin cewa "jama'ar duk duniya tamkar iyali daya ne". Saboda haka, muna fatan samun jin dadin zama, kuma muna fatan jama'ar kasashe daban daban su ma za su ji dadin zaman rayuwarsu. Yanzu haka, yake-yake da talauci na ci gaba da addabar wasu kasashe da yankuna, yayin da mutane da yawa suna jin radadin cututtuka da bala'u daga indallahi. Ganin haka ya sa nake fata, gamayyar kasa da kasa za su hada hannu, su tsaya kan ra'ayi na hadin kan duniya don makomar bil adama, ta yadda za mu raya duniyarmu don ta zama mai cike da zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadata.

Bari mu sanya buri mai kyau, mu jira zuwan sabuwar shekara tare.

Na gode.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China