in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Burundi sun cafke 'yan jaridu 2 da ake zargin shirya shirin lalata shaidu
2016-10-24 10:08:08 cri

Yan sandan kasar Burundi sun sanar a ranar Lahadi da cafke 'yan jaridu biyu, 'yar asalin Amurka guda da wani ma'aikacin gida dake yiwa BBC aiki, ana zargin su da shirya makarkashiya domin lalata shaidu.

Julia Steers, 'yar Amurka, da Gildas Ihundimpundu, 'dan jaridar Burundi, dake yiwa BBC aiki, an kama su a Mutakura, a yayin da suke daukar hotuna na wani kabarin gama gari, in ji kakakin 'yan sandan Burundi, Pierre Nkurikiye.

Ana zargin su da shirya shirin latata wasu shaidu na cewa, mahara sun kashe mutane, da kuma jefa su cikin kabari guda, in ji mista Nkuririye.

Kakakin ya bayyana cewa, 'yan jaridun biyu ba su sanar da hukumomi ko 'yan sandan wurin game da zuwansu a Mutakura, dake arewacin babban birnin Bujumbura.

Burinsu shi ne na lalata shaidu na cewa mahara sun kashe mutane, kana suka jefa su cikin kabari guda can, in ji mista Nkuririye.

A cewarsa, masu bincike da wakilan kwamitin harkokin yada labaru na Burundi CNC suna jiran 'yan jaridan biyu.

Shugaban CNC Ramadhan Karenga ya bayyana cewa, an saki 'yar jaridar Amurka jim kadan bayan da CNC ya tabbatar da takadar shaidarta.

An saki 'yar jaridar Amurka, amma 'dan jaridar Burundi har yanzu yana hannun 'yan sanda bisa dalilin cewa, babu sunansa cikin jerin sunayen 'yan jaridu dake hannun CNC, in ji mista Karenga. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China