A jiya Larabe ne majalisun dokokin kasar Burundi suka kada kuri'ar ficewa daga kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya(ICC)
Ministan shari'a na kasar Burundi Aimee Laurentine Kanyana wanda ya halarci zaman kada kuri'ar ficewar, ya ce, kasar Burundi ta fice daga kotun ne, saboda ba abin da kotun ta ke yi, illa yaki da kasashen Afirka.
Yayin da jam'iyyar CNDD-FDD mai mulki ta ke kallon matakin ficewa daga kotun a matsayin wanda ya dace, su kuma 'yan majalisun da ke adawa da gwamnati, sukar lamarin suka yi, suna masu cewa, mataki ne da ba za a hukunta masu aikata manyan laifuffuka ba.
A makon da ya gabata ne, mataimakin shugaban kasa na daya Gaston Sindimwo ya sanar da cewa, Burundin ta yanke shawarar ficewa daga kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) saboda 'yan Afirka kawai ta ke hukuntawa.(Ibrahim)