in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukuni na biyu na 'yan tawayen Syria sun bar Aleppo
2016-12-16 11:02:58 cri

Rahotannin baya bayan nan na cewa, rukuni na biyu na dakarun 'yan tawayen Syria ya bar yankin arewa maso gabashin birnin Aleppo a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na SANA ya bayyana cewa, tuni rukunin farko na dakarun tare da iyalan su suka isa Rashidien dake wajen yammacin birnin na Aleppo, matakin da ya sanya yawan wadanda suka bar arewa maso gabashin birnin kaiwa mutane 1,150.

Ana sa ran yawan mutanen da za su fita daga wannan yanki na Aleppo zai kai mutane 15,000, ciki hadda 'yan adawa 4,000, karkashin yarjejeniyar da Rasha da Turkiyya suka kulla.

An dai ga motoci kirar Bas na kwashe dakarun da iyalan su daga yankin da yammacin ranar ta Alhamis, yayin da kuma motocin daukar masara lafiya suka yi jerin gwano dauke da wadanda ke bukatar kulawar jami'an lafiya. An kuma ce hakan na gudana ne karkashin jagorancin kungiyar jin kai ta Red Cross kadai.

Karkashin yarjejeniyar dai 'yan adawar za su mika makaman su, yayin da a daya hannun za a tabbatar da cewa, sassan biyu sun kauracewa sake kaiwa juna hare-hare. Kaza lika yayin da 'yan adawar ke barin gabashin Aleppo, a nasu bangare za su kyale fararen hula dake lardin Idlib su fita daga garuruwan 'yan Shi'an nan na Kafraya da Foa da aka yiwa kawanya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China